Shekaru 15 na Jagoranci: Kakakin Majalisar Bauchi Ya Taya Sarkin Bauchi Murnar Cika Shekaru 15 a Kan Karagar Mulki
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Rt. Hon. Dr. Abubakar Y. Suleiman (Dangaladiman Ningi), ya taya Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji (Dr.) Rilwanu Sulaiman Adamu, murnar cikarsa shekaru goma sha biyar (15) a matsayin Sarkin Bauchi, yana mai bayyana shi a matsayin ginshikin hadin kai, zaman lafiya da cigaban al’umma. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Garba Kobi, ya fitar, Kakakin Majalisar ya jinjina wa irin kyawawan halaye da nagartattun shugabanci da Mai Martaba Sarki ke nunawa, musamman a kokarinsa na wayar da kan matasa wajen koyon sana'o’i da kuma yada sakon zaman lafiya. Ya ce Sarkin Bauchi mutum ne mai tausayi da sadaukar da kai ga tallafawa marasa karfi ba tare da la’akari da kabila, yare ko addini ba. Haka kuma, kokarinsa na inganta tarbiyya ya haifar da sabuwar al’umma mai gaskiya, jajircewa da hangen nesa. “Sarkin ginshiki ne wajen dawo da dabi’un al’umma na kwarai, da tarbiyya mai kyau da kuma girmama doka da oda,” in ji Kakakin Majalisar. Ya kara d...